26 Afirilu 2022 - 19:14
Majalisar Dinkin Duniya Tana Tsammanin Cewa; “Yan Gudun HIjirar Ukiraniya Za Su Kai Miliyan 8 A wannan Shekarar

Mai magana da yawun hukumar ‘yan gudun hijira ta MDD, Shabia Mantoo ta bayyana a yau Talata cewa; A wannan shekarar adadin ‘ya gudun hijira daga kasar Ukiraniya za su kai miliyan 8 da dubu dari uku.”

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mantoo ta kara da cewa; Da akwai mutane miliyan 12.7 da suka gudu daga gidajensu a cikin watanni biyu da su ka gabata, daga cikinsu da akwai miliyan 7.7 da su ke a cikin gida, yayin da wasu miliyan 5 suka ketara iyaka.

A baya MDD ta yi hasashen cewa za a sami ‘ yan gudun hijira miliyan biyar ne daga kasar Ukiraniya, sai dai tun a cikin watan Maris ne adadin ‘yan gudun hijirar ya haura hakan.

Shi kuwa Asusun MDD na kananan yara, Unicef, ya bayyana cewa; Rabin mutane miliyan 7..5 na ‘yan gudun hijirar Ukiraniya kananan yara ne.

Har ila yau, Mantoo ta bayyana cewa; Babbar matsalar ‘yan gudun hijira da ake fuskanta a duniya ita ce ta kasar Syria inda ake da fiye da ‘yan gudun hijira miliyan.6.8.

342/